Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Giodano dake jihar kano a arewacin najeriya yace sabon tsarin bunkasa cigaban matasa da kungiyar Giodano ta shirya a karo farko a tarihi zai bawa kungiyar damar daukar nauyin yan wasan da sukayi nasarar samun zuwa gwaji a kasar jamus daukar nauyin su batare da sun biya ko sisi ba,
A tattaunawarsa da Express Radio 90.3 fm a jihar kano Jamilu Wada ya bayyana dalilin kawo turawan daga kasar jamus da cewa wata hanya cewa wata sabuwar hanyace da kungiyar zata budewa matasan jihar kano da wasu jihohi na arewacin kasarnan dan samun damar da marasa karfi dake da basirar kwallon kafa basu da ita inda yace ” Mun shirya wannan wasan gwajin da zabin yan wasane badan kungiyar mu kadai ba sai dai dan mu bawa matasan jihar kano damar fito da basirarsu ko Allah zaisa wasu su dace mu kuma mu shiga gaba dan ganin sun samu shiga ba tare da mun karbi ko kwabo ba”
Dayake amsa tambaya kan ko wannan gwaji na had in gwiywane ko kuwa Jamilu Wada cewa yayi babu hadin gwiywa da kowa kungiyar Giodano ce kadai ta dauki nauyi kuma itace zata dauki nauyin duk dan wasan da yayi nasarar samun zuwa gwajin,
Dan gane da yawan kungiyoyin da zasu shiga wannan atisaye Jamilu Wada cewa yayi mun gayyaci kungiyoyi sama da 20 a karon farko kuma muna fatan a samu yan wasan da ake bukata da shiga ko tafiya wannan gwaji kasar jamus,
Dayake karin haske kan yan wasan da zasu chanchanci shiga Jamilu Wada cewa yayi shekarun yan wasa daga 18 zuwa 20 da yan 23 ne ake bukata a wannan haka kuma akwai yiwuwar mu sake gayyato su a karshen shekara dan duba matasan yan wasa daga shekaru 15 zuwa 16 kuma duk Giodano ce zata dauki nauyi,
Kan yadda yan wasan zasu sami tafiya zuwa gwajin shugaban cewa yayi na fada na sake fada duk dan wasan da aka dauka wato ya samu chanchantar zuwa gwaji zai tafine da sunan Giodano kuma mu zamu dauki nsuyinsa bayan mun tattauna da shugabanninsu, abinda muke bukata shine mu samu invitation na yaron mu kuma mu biyamasa kudin Tikiti, Jirgi da komai da komai fatan mu kawai yaran mu na kano su sami dama mukuma mu taimaka masa, da duk abin da zamu iya,