Babban daraktan Cibiyar wayar da kan al’umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci (CAJA), Comrade Kabiru Sa’idu Dakata ya yi wata wallafar wani rubutu a shafinsa na facebook mai taken “Banbance – banbancen da ke tsakanin videon Faruk Lawan da na mu videon”
A cikin rubutun da Kabiru Dakata din ya yi ya jero wasu banbance guda huɗu da ke tsakanin bidiyon Farouk Lawan da kuma wanda ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne a ciki yana karɓar Dalolin Amurka.
Ga banbancin da ya rubuta a shafinsa:
-A wurin kyan video, na Faruk Lawan ya yi dishi – dishi kamar talabajin black and white, na mu kuwa ya fito garai garai tamkar allon cinema.
Dollar Faruk a ambulan aka mika ta, ta mu kuma tsirarar dollar ce sinki sinki.
Faruk shi ya je ya karba, mu kuma kawo mana aka yi.
Dollar Faruk ta shafi cin hancin tallafin man fetir, ta mu kuma ta shafi cin hanci domin dakile duk wani nau’i na ci gaban al’umma.
A cikin shekarar 2018 ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a shafukan intanet ta saki wasu jerin bidiyo da hasko fuskar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar makudan Dalolin Amurka.
Sai dai tuni gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya musanta cewa ba shi ne a cikin bidiyon