Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Tarayya ta raba naira biliyan 605.958 tsakanin ita kan ta, gwmnatocin jihohi da kuma ƙananan hukumomi 744 na ƙasar nan.

Wannan adadi da su ka kasafta a tsakanin su, ya gaza ga wanda su ka raba a watan Afrilu da naira biliyan 69.

Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafi Da Tsare-tsare, Charles Nwodo ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce an tara kuɗaɗen daga harajin kwastan, cinikin fetur da kuma na Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Cikin Gida (FIRS).

“Gwamnatin Tarayya ta karɓi naira biliyan 242.120, Jihohi 36 sun karɓi naira biliyan 194.195. Sai kuma Ƙananan Hukumomi aka kasafta masu naira biliyan 143.742.”

Sannan kuma an ƙara lafta wa jihohi masu arzikin man fetur Naira biliyan 26.901.

Nwodo ya kuma ce a cikin kuɗaɗen harajin da aka tara, naira biliyan 181.078 harajin jiki mahayi ne, wato VAT.

Sannan ya ce harajin VAT ɗin da aka tara a Mayu, ya fi wanda aka tara a watan Afrilu, inda aka tara naira biliyan 176.710 a Afrilu ɗin.

Waɗannan maƙudan kuɗade da Najeriya ke rabawa duk ƙarshen wata, ba su hana ƙasar fafurikar neman bashi ba a kullum.

Sannan kuma har yanzu ba su sa Najeriya ta fita daga ƙangin ƙuncin rayuwar talakawa ba.

Ko a ranar Laraba ƙasar Canada ta bai wa Najeriya tallafin dala biliyan 27, domin agaji ga yankin Arewa maso Gabas, yankin da Canada ta ce ya na cikin yankin da ke sahun gaban masu fama da ƙuncin rayuwa da ‘yan gudun hijira a duniya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *