Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Babban Hafsan sojojin Nijeriya ya kai ziyara jihar Imo, inda ya bada umarnin a ragargaji yan IPOB.

Janar Faruk ya ce manufar ziyarar tasa itace tantance yanayin tsaro a jihar ta Imo da kewayenta.

Jihar Imo ta fuskanci hare-hare da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne ke kai wa jama’a a kwanakin da suka gabata

Janar Faruk Yahaya, ya kuma nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro a jihar.

An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam’iyyar APC, Ahmed Gulak.

A wata sanarwa da majiyar mu ta samo daga Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar, ya ce babban hafsan sojojin ya kuma jinjina wa sojojin saboda juriyar su.

Babban hafsan sojan kasa (COAS) Manjo Janar Faruk Yahaya ya yaba wa irin karfin gwiwa da kokarin sojoji na Brigade 34 da sauran jami’an tsaro wajen juya akalar rikice-rikicen rashin tsaro na baya-bayan nan wanda ya samo asali daga ayyukan ta’addanci na kungiyar IPOB, a jihar Imo.

Da yake yaba nasarorin da rundunar ta samu, ya kuma bukace su da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankin.

Wani yankin sanarwar na cewa: “COAS ya nuna farin ciki kan nasarorin da sojojin suka samu ya zuwa yanzu kuma ya bukace su da su rubanya kokarin su domin karfafa nasarorinsu.

Janar Yahaya ya kara da umartar su da su kasance masu biyayya da nuna kwazo a kowane lokaci. Ya yi nuni da cewa, za a samu karin nasarori ta hanyar bin umarni da biyayya.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *