Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Masarautar Bichi da ke jihar Kano ta yi jaje ga wadanda suka kamu da cutar kwalara a karamar hukumar Bichi.

Sarkin masarautar Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero ya ce yana cikin damuwa game da barkewar mummunar cutar.

Babban basaraken a cikin wata sanarwa da sakataren majalisar masarautar, Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai ya fitar ya bayyana cewa Sarkin wanda ba shi da sani, lokacin da abin ya faru ya yi gaggawar sanar da ma’aikatar lafiya ta jihar da sakataren Gwamnati jihar don hanzarta ɗaukar matakan tallafawa domin bada magani.

Sarkin ya nuna damuwar sa tare da tabbatar da cewa masarautar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman samar da isassun kayan magani domin jindadin jama’a ga yankin sa.

Ya ce shi da kansa yana neman karin zabi ta hanyar gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da nufin zuwa don ganin karshen cutar yankin masarautar.

Sarki Nasir Ado Bayero ya bukaci al’ummomin yankinsa da su yi koyi da kyawawan hanyoyin tsaftace muhalli.
Ya kara da cewa yin riko da mafi kyawun tsabta zai taimaka masu sosai da kuma kiyaye su daga wasu cututtukan makamancin wannan.

Ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da ba wadanda suka kamu da cutar lafiya tare da jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu yayin annobar.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye faruwar lamarin a nan gaba.

Sanya hannu:
Sakataren Masarautar Bichi,
Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *