Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar tsaron farin kaya DSS ta bayar da belin mawakin nan Ahmad Abdul da ake zargin ya yi kalaman batanci ga Allah a Jihar Kano.

Hukumomi sun ce an bayar da belin nasa ne bayan ya nemi afuwar al’ummar jihar da daukacin Musulmin duniya kan wakar da ya yi.

Hukumar ta DSS ta shaida wa manema labarai cewa an kama mawakin mai shekara 35 bayan ya fitar da wakar ba tare da hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jihar Kano ta tantance ta ba.

A cewar hukumar ta DSS, an tsare shi ne domin kauce wa tashin hankali da kai wa matashin da iyayensa hari a sakamakon wakar da ya yi,

Sai dai ta kara da cewa matashin ya amsa laifinsa bayan hukumar tace fina-finan ta jihar Kano ta nuna masa illar abin da ya yi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *