Carlo Ancelotti bai bata lokaci bayan komawarsa Real Madrid daga Everton, dan kasar Italiyan ya riga ya je aiki a Valdebebas. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Ancelotti ya sanya hannu kan kwantiraginsa a Real Madrid a ranar 2 ga Yuni kuma, duk da ci gaba da buga Gasar cin Kofin kasashen Turai da kuma tun kafin fara kakar wasanni har yanzu da dan sauran lokaci, ya fara aiki a harabar kungiyar.
‘Yan wasan Real Madrid – wadanda ba bugawa kasashen su na duniya wasa – za su sake dawowa bayan makwanni biyu, a ranar 5 ga watan Yuli. Sauran za su dawo ne a hankali dangane da yarjejeniyar da suka cimma da kocin.
Kociyan dan Italiyan ya fara aiminsa a karo na biyu a matsayin kocin Real Madrid kuma yana da aiki da yawa a gabansa. Yan wasan yanzu suna bukatar wasu ayyuka a wannan bazarar, kuma dole ne a yanke shawara game da yawancin ‘yan wasan 29 da yake da su a halin yanzu.