Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wasu masu zanga-zangar, a safiyar ranar Litinin, sun tare hanyar Umaru ‘Yar Adua Way da ake zuwa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Masu zanga-zangar wadanda ke nuna tutoci dauke da rubutun, #BuhariMustGo, sun mamaye yankin da misalin karfe 5:30 na safe.

A cewar rahotanni, masu zanga-zangar sun yi ta cinna wuta a kan hanyar da ke cike da mutane, lamarin da ya sa ya zama da wahala ga ma’aikatan gwamnati da ke zaune a Lugbe, Kuje, da sauran yankunan da ke kusa da Filin jirgin saman samun damar zuwa wuraren aikin su a tsakiyar garin.

Wani dan rajin kare hakkin dan adam na Najeriya, Omoyele Sowore ya bayyana ci gaban a shafinsa na Twitter.

Tweeter din ya karanta, “Masu zanga-zangar #BuhariMustGo sun toshe hanyar zuwa filin jirgin saman kasa da kasa a Abuja tun da karfe 5:30 na safiyar Litinin a Abuja #RevolutionNow”.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda na FCT, Mariyan Yusuf ba ta iya daukar wayarta ba kuma ba ta iya amsa sakonnin tes da aka turo mata ba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *