Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Fc ta ce kulob din ya kammala dukkan shirye-shirye don tabbatar da cewa dan wasanta Auwalu Ali Malam da aka gayyata zuwa sansanin Super Eagles a gabanin wasan sada zumuncin da za su kara da Mexico a watan gobe komai ya zo a kan lokaci. Fagenwasanni.com ta rahoto.
A cewar jami’in yada labarai na kungiyar Rilwanu Idris Malikawa ya ce shugabannin karkashin jagorancin Alhaji Surajo Shaaibu Yahaya jambul sun yi farin ciki da wannan ci gaban kuma sun yi alkawarin ba da goyon baya da kwarin gwiwa ga Auwalu Ali Malam da kowane dan wasa a cikin kungiyar don samun nasarar gayyatar anan.
Malikawa ya ce shuwagabannin suna taya Auwalu Ali Malam murna kuma sun bukace shi da ya zama kyakkyawan jakada daga sai masu gida,
gwamnatin jihar Kano da masoya wasan kwallon kafa na jihar Kano suna yi masa fatan alkhairi a duk inda ya samu kansa.
Gayyatar daya daga cikin ‘yan wasan mu daga cikin’ yan wasan gida ashirin da biyar zuwa kungiyar ta kasa abin alfahari ne ga kungiyar da kuma jihar Kano baki daya kuma muna da kwarin gwiwar cewa wasu ‘yan wasan mu za su kasance cikin kungiyar kasar nan ba da jimawa ba, in ji Malikawa.
Malikawa ya ce Auwalu Ali Malam zai kasance a sansanin gobe kamar yadda NFF ta nema kuma muna yi masa fatan alheri da Super Eagles gabadaya.