Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya Sheakh Musa Ayuba Lukuwa ya bayyana cewar, da ikon Allah gwamna Aminu Tambuwal ba zai sami nasarar cin zaben kujerar shugaban kasa a 2023 Ba.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a cikin Babban masallacin sa da yake gudanar da huduba a unguwar Mabera anan birnin Sokoto.

Malamin ya ce, aikin su daga yanzu su tashi tsaye ba dare ballai rana don rokon Allah kada ya baiwa gwamna Aminu Tambuwal nasarar zama shugaban kasar.

“Sai dai mu ce, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un duk lokacin da aka bayyana cewar Aminu Waziri ya zama shugaban kasar nan domin mun shiga ukku”~ inji malamin

Babban malamin mai dinbin mabiya ya bayyana cewar, dukkanin malamai da limamai su dukufa da addu’a don ganin gwamna Tambuwal bai sami nasarar cin zaben 2023 Ba.

“Ai gwanda Buhari nesa ba kusa ba da wanga gwamna namu na jihar Sokoto Aminu Tambuwal”~ inji shi

Daga Jaridar Sokoto

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *