Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun mutane sun cinnawa wata babbar mota mallakar kamfanin siminti na Dangote, Ibese, da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun wuta bayan ta murkushe wasu maza biyu har lahira.

Direban motar an ce da kyar ya tsere daga sashin sa.

Majiyarmu ta labarta mana cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a kan hanyar Igbogila-Ilaro

An gano cewa mutanen biyu suna kan babur ne, daga Igbogila zuwa Ilaro lokacin da lamarin ya faru.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa direban motar Dangote ya kauce daga layinsa, inda ya yi karo da babur din da ke tafe wanda aka fi sani da okada.

Kakakin TRACE, Babatunde Akinbiyi, ya ce, “kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar, direban babbar motar Dangote ya yi tukin ganganci. Ya bar layinsa don fuskantar mai babur din da fasinjan fasinjan a bayansa a daya layin ya murkushe su har lahira.

“Wasu mutane da suka fusata sun bankawa motar Dangote wuta a yayin da direban ya gudu. Ofishin ‘yan sanda na Kamfanin Dangote ne ke kula da lamarin.”

Akinbiyi ya kara da cewa daya daga cikin gawarwakin wadanda suka mutu an ijiye a dakin ijiye gawarwaki na Babban asibitin Ilaro, yayin da dayan mamacin aka riga aka binne shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *