Faruk Yahaya ya sanar da haka a jiya lokacin da ya bayyana a gaban hadakar kwamitin majalisar wakilai na tsaro da sojoji domin a tantanceshi a Abuja.
Yace yana sa ran amfani da kwarewarsa ta shekaru 36 a aikin soja wajen aiki tare da sauran hafsoshin soja domin magance matsalar tsaro a kasarnan.
Faruk Yahaya yace yana da dukkan abubuwan da ake bukata domin magance kalubalen tsaro a kasarnan, idan aka yi la’akari da gogewarsa.