Jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar ƴan Sanda a Jihar ta Ogun, Abimbola Oyeyemi shine ya tabbatarda hakan yayin zantawa da manema labaru ayau Lahadi.
Mahaifin yaran guda biyu da aka cefanar mai suna Oluwaseyi Agoro shima ya bayyanawa manema labarai cewa “yayi tafiya na tsawon wani loƙaci abin takaici dawowar sa ke da wahala ya riski labarin cewa matarsa ta cefanar da yaran guda biyu.
Har’ilayau; ya kuma ƙara da cewa “tun bayan sanin cewa yaran nasa basa gida, dafarko yayi ƙoƙarin tuhumar matarsa domin sanin wurinda suka shiga amma ta yi kunnen uwar shegu, dalilin da ya sanya kenan harya shigar da ƙara izuwa ofishin ƴan Sanda domin sanin irin yanayin da yaran suke ciki.
A gefe guda, yayin tuhumar matar da ake zargi da wannan aika-aika? ta tabbatarda cewa mijin nata mai suna Oluwaseyi Agoro ya bar gida sama da tsawon shekaru biyu, kuma ba tare da waiwayar halin da take ciki da ƴaƴanta ba “dalilin kenan da har ya sanya ta yanke shawarar cefanar da yaran domin samun abinda zata ɗauki ɗawainiyar ragowar ƙananan yaran nata.