Gwamna jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce bai samu damar yi wa al’ummar jihar Borno ayukkan ci gaba ba a mulkin sa ba.
Gwamnan ya ce matsalar tsaro da jihar take fama da ita yana daga cikin matsalolin da suka hana shi yi wa jihar abubuwan cigaba.
Dudda yake Gwamnan ya gabatar da manyan ayukka 556 wadanda ya gudanar a cikin wannan yanayi na matsalar tsaro.
Amman dudda haka Gwamnan ya ce bai yi wa al’ummar jihar sa komai ba, kuma yana neman afuwar su.