Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, ya bi sahun masu zanga-zangar a Ibadan, babban birnin jihar.
A wani bidiyo mai dauke da hoto da Jaridar Mikiya ta gani, ana iya ganin Seyi Makinde cikin shigar kaya ruwan ƙasa a cikin mota, yana ɗagawa matasa hannu.
Bugu da ƙari a cikin yanayin murna da ihun yabo kafin ya yi musu jawabi.
Masu zanga-zangar suna nuna adawa ne da rashin shugabanci na gari, rashin tsaro, da kuma adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari.
Zanga-zangar ranar dimokiradiyya na gudana a kewayen Najeriya duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na dakatar da yunƙurin.
Daga Lagos zuwa Ibadan, Akure, Oshogbo har ma da Abuja, masu zanga-zangar, akasari matasa, sun fito zanga-zangar ne yau a fusace.