Shugaban Rundunar kare Afkuwar hadura ta kasa shiyar jihar Kano Zubairu Mato yace laakari da yadda wasan tseren kekuna ke dashi na Inganta lafiya da samar da halin kai da bunkasa tattalin arziki da samar da sana’a ga matasa hukumarsa zata sanya gasar tseren kekuna nan bada dadewaba a jihar Kano.
Da yake tabbatar da haka ga wakilinmu a yayin da shugabannin hukumar tseren kekuna suka kai masa ziyarar gidiya bisa irin gudummawar da yake bawa mahaya kekuna a jihar Kano, kwamandan rundunar Zubairu Mato yace hukumar ta yanke shawarar sanya gasar ne dan zaburar da alummar wajen yin amfani da kekuna wajen sufuri da tafiye tafiya tsakanin gurare inda yace hakan zai taimaka matuka wajen inganta lafiyar alumma musanman manyan mutane masu shekaru
Da yake karin haske kan gasar Mato cewa yayi hukumarsa zata samar da kofina 3 inda zaa bawa na 1 ,2 dana 3 da sukayi fice, kan inda zaa gudanar da gasar shugaban runfunar kare haduran ta jihar kano cewa yayi inda zaayi tseren ya dogara ne da inda shugabannin kungiyar tseren kekunan suka zaba,
Tsohon dan hukumar kwallon hannu Mato kara da cewa akwai bukatar masu hannu da shuni da kamfanoni su tallafawa harkokin wasanni a fadin kasarnan inda yace hakan zai taimakawa kasa wajen samar da ayyukanyi ga matasa da hada kan alumma,
Zubairu Mato wanda a farkon makon ji ya jagoranci bikin ranar hawa keke ta duniya inda da Kansas ya tuka keke zuwa hukumar wasanni ta jihar kano yace yayi hakanne dan nunawa mutane irinsa cewa girma ko mukami ko wadata basa hana hawa keke.