Kasar Amurka tayi kira ga Gwamnatin Najeriya data tsare rayukan Yan Jarida a Najeriya, inda tace Yan Jarida na fuskantar barazana a rayuwar su.
Jami’in Harkokin Jama’a na Amurka Stephen Ibelli ya bayyana haka a lokacin dayake jawabi a kafar Sadarwa ta Zoom a Uyo, a lokacin taron horaswa na Yan Jarida masu binciken kwakwaf da kawo rahotannin lafiya, wanda cibiyar jarida ta Duniya dake da reshe a yankin Kudu maso Kudu hadin gwuiwa da kasar Amurka.
Yace Yan jarida na aiki a kasar nan akan yanayi marar dadi.
Ya kara dacewa Amurka zata taimakawa masu bincike akan lafiya, inda yace tuni ta dade tana bayar da gagarumar gudunmuwa wajen daukar nauyin shirye-shiryen lafiya a kasar kamar irin su Hukumar USAID.
Ibelli “na yaba da wannan cibiya data hada hannu damu. Tare da nuna sha’awar kawo rahoto akan kiwon lafiya.