Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dr Isa Pantami, ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, ya ce bullo da NIN ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga – Pantami ya yi wannan ikirarin ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke bayanin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu tun fara aikinsa a 2019.

Kamar yadda kamfanin yada labarai na Legit Hausa ya rawaito, Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Dr. Isa Pantami ya yi ikirarin cewa tsarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bullo da shi na tursasawa yan Nigeria mallakar lambar yan kasa wato NIN, ya rage garkuwa da mutane da harin yan bindiga, The Punch ta ruwaito. Tribune ta ruwaito cewa Pantami ya yi wannan ikirarin ne a Abuja, a ranar Alhamis, yayin da ya ke bada ba’asi kan nasarorin da ya samu tun fara aiki a shekarar 2019.

Ya ce, “Lokacin da aka nada ni in jagoranci sashin a ranar 24 ga watan Agustan 2019, ana amfani da katin waya wadanda ba a yi rajista ba ko wadanda ba a kammala rajistan ba wurin aikata laifuka. Babu wanda ya san adadin layukan waya marasa rajista.

Cikin kwanaki 15 da kama aiki, mun tuntubi NCC a matsayinsu na masu kula da harkar. Mun umurci suyi bincike su gano adadin layin waya marasa rajista. Sun gano miliyan 9.4 wanda ya kai adadin mutanen wasu kasashen. Wannan ne karo na farko da muka san adadin layukan waya marasa rajista a kasar nan. Pantami ya ce daga nan ya umurci NCC ta tabbatar da cewa layukan wayoyi masu rajista na kwarai ne kawai za su rika aiki a kasar kuma an cimma hakan zuwa Satumban 2021.

Daga Satumban 2019 zuwa 2020, za ka lura cewa an samu saukin garkuwa da mutane da harin yan bindiga. A baya da wuya a yi wata daya ko fiye ba tare da ka ji labarin garkuwa da mutane ba. “A yayin da ka ke kokarin dakile hanyoyin da miyagu ke amfani da su wurin aikata laifi, miyagun za su rika bullo da sabbin hanyoyi.”

Mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta ya ce a yanzu masu garkuwa na amfani da wayoyin wadanda suka sace ne domin karbar kudin fansa amma ya ce gwamnati na aiki don ganin yadda za ta magance lamarin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *