Wani matashi Umar Ibrahim Tamburawa dake Yankin karamar hukumar dawkin kudu yace bashi da abin alfahari daya wuce kwakwalwa da Allah ya bashi,
A wata tattaunawa da yayi da wakilin mu Umar yace bayan lafiya da Allah yake bashi yana amfani da kwakwalwarsa wajen yin gogayya da wadabda suka shahara wajen kirkire kirkire a fannin zane zanen gine gine da zaayi alfahari dasu a fadin. Duniya, Umar wanda dalibine yanzu haka a makaratar fasahar mahalli dake garin gwarzo ya kirkiri wani kata faren Hotal da gurin cin abinci da yace wajen da zai dauki hankalin alummar daniya musamman masu bukatar shakatawa da son daukar hoto a guri mai kyau
Inda Umar din yace wannan gurin daya kirkira yayishine bayan zurfin tunani inda yace wajena dake da babbar haraba da zai iya daukar matoci 50 a lokaci guda kuma wani abu daya zama sabo shine samar da wajen shakatawa a saman ginin kamar yadda yake a kasa abin da Umar din yace sabon abune a tsarin gine gine,
Matashin wanda da alamu fasaha ta cika kansa nada burin samarwa alumma kirkire kirkire da zasu daga darajar kasar mu inda ya ja hankalin matasa dasu dukufa wajen neman Ilimi dan samun makoma me kyau da samun abin dogaro,