Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci dukkan mazauna jihar da su mika makaman da suka mallaka ba bisa ka’ida ba ga hukumar ‘yan sanda mafi kusa dasu a cikin kwanaki bakwai kacal.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne yayin saka hannu a wata takardar shela ga dukkan jihar Zamfara, kamar yadda hadiminsa a harkar yada labarai, Zailani Bappa ya sanar a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar ta nuna, umarnin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bada na harbe duk wanda aka kama da makamai ba bisa ka’ida ba a take, Daily Nigerian ta ruwaito.

Takardar ta ce: “Domin tabbatar da karfin ikon da nake da shi, ni Dakta Bello Mohammed, ina bada wadannan umarnin.

“Dukkan makamai dake hannun jama’ar jihar Zamfara ba bisa ka’ida ba, a mika su ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa a cikin kwanaki bakwai daga ganin wannan sanarwan,” takardar ta sanar da hakan.

Bappa ya kara da cewa, gwamnan yayi kira ga mazauna jihar da su kasance masu kiyaye doka domin samun damar shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *