Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Jihar Ondo da ke Najeriya Rotimi Akeredolu ya bukaci soke Majalisar dattawan kasar domin rage kudaden da gwamnati ke kashewa akan ‘yan siyasa.

Akeredolu wanda tsohon shugaban lauyoyin Najeriya ne ya kuma bukaci mayar da zaman Majalisar tarayya ya zaman a wucin gadi maimakon na din-din-din a kasidar da ya gabatarwa taron nazarin kundin tsarin mulkin kasar da ke gudana yanzu haka.

Gwamnan ya ce abinda ya gabatar shi ne matsayin gwamnatin jihar Ondo inda suka bukaci rage nauyin da ke kan gwamnatin tarayya da kuma bukatar ganin kwazon jami’an gwamnati a aikace wajen inganta rayuwar jama’ar kasa.

Akeredolu ya ce bukatar Jihar Ondo ta kunshi mayar da aikin majalisa na wucin gadi da kuma dakile kashe kudaden da hukumar tara kudaden haraji ta kasa bata san da zaman su ba musamman akan mutanen da ke ikrarin yiwa kasa aiki.

Gwamnan ya ce bayan soke Majalisar Dattawa, ya dace a sanya mutane akalla 4 daga kowacce shiyya domin wakilci a majalisar wakilai. Yanzu haka Najeriya na da ‘yan Majalisu 469 da suka hada da ‘yan Majalisun Dattawa 109.

‘Yan Najeriya sun dade suna korafi kan irin makudan kudaden da ake kashewa Majalisun Tarayyae kuma duk wani kokari na rage kudin ya ci tura.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *