Yanzu-yanzu ‘yan bindigar suka sace dalibbai kusan 200 a makarantar Salihu Tanko dake garin Tegina sun bukaci da a biya kudinsa wadannan dalibbai daga yau zuwa gobe ko kuma su hallaka su.
‘Yan bindigar sun bukaci da a basu Naira miliyan 110 a matsayin kudin fansar wadannan daga yau Talata zuwa gobe Laraba ko kuma su bindige wasu daga cikin su.
Shugaban makarantar ta Salihu Tanko ne ya bayyana hakan jim bayan da ya kira su barayin a yau.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ya baiwa jami’an tsaro umurnin gaggauta ceto wadannan dalibbai ne.