Ministan Sadarwa da raya Tattalin Arzikin zamani na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya kaddamar da manyan ayyukan farfado da tattalin Arziki guda Biyar a wasu jihohin Nijeriya.
Ga jerin ayyukan kamar haka:-
1. National Policy on Virtual Engagements in the Federal Public Institutions.
2. Cibiyar Sadarwa ta Gaggawa, dake Akure, Jihar Ondo.
3. Cibiyar Tattalin Arzikin zamani, dake Jami’ar Tarayya ta Gashua, Jihar Yobe.
4. Cibiyar Tattalin Arziki ta Digital, dake Jami’ar Jihar Delta ta Abraka, Jihar Delta.
5. Cibiyar Tattalin Arziki, ta Secondary School Rigasa (Main), dake Jihar Kaduna.
Ministan Sadarwa Sheikh Pantami, ya kaddamar da ayyukan ne a karkashin tsarin farfado da tattalin Arziki na #DigitalNigeria.