Gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike ya gargadi kungiyar IPOB da cewa kada su kuskura su tsallaka jihar sa da sunan kafa wata doka, domin jihar Rivers baza ta dauki wani shashanci ba.
Gwamnan ya ci gaba cewa” Tun da dadewa na haramta kungiyar IPOB a jiha ta ta Rivers, kuma yau na sake nanatawa cewa na haramta ta, na haramta ta, kuma ta haramtu”.
“Bazan hana wasu Gwamnonin kudu su sakarwa kungiyar mara ba, amman ni a jiha ta ta Rivers bazan dauki wannan shashanci ba”.
“Saboda haka a shirye nake na dauki kowane irin mataki ne akan kungiyar IPOB matukar suka yi gangancin shiga jiha ta ta Rivers”. Inji Gwamna Wike.
Kungiyar dai ta IPOB na kara kai hare-haren ta’addanci tare da kisan al’umma a cikin ‘yan kwanakkin nan, inda ta lashi takobin ganin an raba Najeriya ta kowace hanya.
Wanda yake ko a jiya ma kungiyar ta IPOB ta baiwa wasu jihohin kudu umurnin cewa kada kowa ya fito waje, kuma wannan umurni ya yi tasiri, domin al’umma basu fito ba.
Sai dai a nashi bangare, Gwamna Wike ya bayyana cewa shi kam jihar sa ta Rivers bazata dauki wannan shashanci ba.