Jagoran kafa kasar Biafara ya yi godiya ga al’ummar wasu jihohin kudancin Najeriya akan bin umurnin da ya bada na kada wanda ya fito a yau Litinin domin tunawa da mutanen da aka kashe a yakin Biafara a shekarun baya.
Nmandi Kanu wanda yanzu haka yake kasar Ingila ya jinjinawa sojojin Biafara da aka kashe a wannan yaki a shekarun baya.
Hakama, a cikin jawabinsa ya lashi takobin tunkarar Gwamnatin Najeriya nan gaba kadan domin kwato ‘yancin kasar Biafara ta hanyar gwabza fada da dakarun gwamnatin Najeriya.
Shin ya kuke kallon wadannan kalamai na Nmandi Kanu ne?