‘Yan kungiyar IPOB sun kashe tsohon alƙalin Babbar Kotun Jihar Enugu kamar yanda suka kashe Dr Ahmad Gulak.
A wani bidiyo da aka wallafa ya nuna yadda ‘yan kungiyar suka zaro Mai Shari’a Stanley Nnaji daga motarsa sannan suka harbe shi a tsakiyar titi, yayin da sauran motoci ke tsaye a bayan tasa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin kudu maso gabas sakamakon umarnin da ƙungiyar ta IPOB mai son kafa ƙasar Biafra ta bayar na zaman gida domin tunawa da ranar yaƙin Biafra.
A kwanan nan, ‘yan kungiyar ta IPOB na kai hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda da na hukumar zaɓe ta INEC tare da kashe al’umma.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Enugu Mohammed Aliyu ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Nasara
Media News