Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyar Manyan Ma’aikata na Jami’o’in Najeriya, ta koka akan karuwar rashin tsaro a Manyan Makarantun Kasar nan, tana mai bayyana cewa babu wani Mamban ta daya tsira.

Shugaban Kungiyar na Kasa Ibrahim Haruna, ya bukaci bayar da lasisin rike bindigu ga masu gadin Jami’o’i a Fadin Kasar nan, inda yace ayyuka sun yiwa jami’an tsaron Kasar nan yawa, musamman ta fuskar shawo kan matsalar tsaro dake fuskantar Kasar.

Haruna yayi wannan jawabin a Abuja a lokacin taron Kungiyar, Wanda ya gudana a cikin ranakun hutu, jim Kadan bayan an sako Ma’aikata da Daliban Jami’ar Greenfield dake Kaduna, wanda aka sace kwanaki 40.

Yace ” mun taru ne domin mu tattauna akan abubuwa da dama, Wanda yafi kowane shine tsaron rayukan mambobin mu da suke aiki a Jami’o’i”

” Muna kira ga Gwamnatin Tarayya data baiwa masu gadin Jami’o’i Wanda suma mambobin Kungiyar mu ne damar rike Makamai, tare da basu horo lokaci zuwa lokaci. Idan akayi haka za’a sami raguwar matsalar tsaro a Makarantu” inji shi.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *