Da sanyin safiyar yau Litanin 31/05/2021, wasu mafusata a gundumar Kurya Madaro dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun datse babbar hanyar zuwa Gusau zuwa Kaura Namoda.
Yanzu haka sun hana matafiya da suka fito daga Sokoto da Katsina da ma wasu kananan hukumomi dake jihar wadanda suka hada da: Shinkafi, Zurmi, Birnin-Magaji, Kaura Namoda da dai sauran wadansu garuruwan dake kan wannan babbar hanyar zuwa babban birnin jiha Gusau.
Haka kuma duk matafiyan da suka fito daga Gusau ba za su wuce Kurya-Madaro ba.
Mafusatan sun dauki wannan mataki ne domin nuna fushinsu ga gwamnati bisa halin ko in kula da suka ce gwamnati ta nunawa al’ummar garin Kurya-Madaro, sakamakon yadda ‘yan ta’adda suke cin karensu ba babbaka kusan tsawon sati biyu ba tare da daukar wani kwakwkwarar mataki ba.
Da yawan mutanen wannan yanki sun rasa rayukansu, dukiyoyinsu da kuma sace wasu da dama domin neman kudin fansa wasu kuma sun zama ‘yan gudun hijira.