Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kakakin Majalisar Jihar Kano, Hamisu Chidari na ɗaya daga cikin matafiya sama da 200 ɗin da Gwamnatin Najeriya ta buga tambarin neman su ruwa jallo, saboda sun ƙi kai kan su a killace bayan dawowa daga tafiya ƙasashen waje, domin gudun kada su watsa sabuwar cutar korona mai saurin kisa a cikin ƙasar nan.

Chidari dai ya dawo Najeriya ne daga Saudiyya, inda ya sauka daga jirgin Ethiopean Airline, a ranar 17 Ga Mayu, 2021 a filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

An ruwaito cewa ya gabatar da takardar shaidar yi masa allurar rigakafin korona ta jabu.

Jami’an kiwon lafiyar Najeriya ne su ka gano cewa takardar shaidar da Chidari ya nuna ta jabu ce, ba gangariya kuma sahihiya ba ce.

Kakakin Harƙallar Rigakafin Jabu:

Majiyoyin da su ka san gaskiyar kwakyariyar da kakakin na majalisar Kano ya tafka, kuma ba su so a ambaci sunayen su, sun bayyana cewa Kakakin Kano ya tafka abin kunya, ya kunyata kan sa, ya kunyata Kano, kuma ya ci mutuncin Najeriya da girmnan kujerar sa.

Ɗaya daga cikin majiyar ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “Daga filin jirgi an ɗauke su kai tsaye zuwa Cibiyar Bunƙasa Harkokin Mata (gini mai kallon Babban Bankin Najeriya, a Abuja), domin a killace su tsawon kwanaki bakwai, sannan a sallame su domin amincewa su cuɗanya da sauran jama’a.

” Amma ana zuwa wurin, sai Kakakin Majalisar Kano ya ce shi dai wurin bai yi masa ba, wai zai tafi ya killace kan sa a Nicon Luxery Hotel, a Abuja. Hukuma ta amince da alƙawarin da ya ɗauka, amma ya ci amana, ya karya wannan alƙawarin, domin ya arce ba a san inda ya ke ba, ballantana jami’an NCDC su riƙa kula da shi.”

Lambar fasfo ɗin Chidari dai ita ce B50022050, kuma sunan sa ne a na 66 a jerin mutum 132 da su ka karya ƙa’idojin da Kwamitin Daƙile Korona ya shimfiɗa.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha shi ne shugaban kwamitin.

Dama kuma tun a ranar 23 Ga Mayu an buga tambarin neman rukunin mutanen farko su 90 da ake nema saboda sun arce ba tare da tsayawa an killace bayan sun shigo kasar nan daga bulaguro a wasu ƙasashe da su ka je ba.

PREMIUM TIMES ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Kano, Chidari, amma abin bai yiwu ba, kuma ba shi da jami’in watsa labarai.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Majalisar Kano, Uba Abdullahi, ya yi ƙoƙarin haɗa wakilin mu da Chidari, amma abin bai yiwu ba.

Shi ɗin ma cewa ya yi, “Kamata ya yi kafin kwamitin ya bayyana sunan Chidari a duniya, kamata ya yi a fara tuntubar Chidarin tukunna.

Jami’in ya nemi wakilin mu ya ziyarce shi a Kano, domin su maganta batun a can.

Ya bada hujjar cewa ma’aikatan majalisa na yajin aiki, shi ya sa duk wani kokarin gudanar da haɗuwa da kakakin ke kasancewa a takure.

Da aka tuntubi Boss Mustapha, Kakakin Yaɗa Labaran sa Willy Bassey cewa ya yi,aikin su kawai idan mutum ya gudu, su fallasa sunan sa kowa ya gani, domin a yi kaffa-kaffa da shi.

Chidari ya zama Kakakin Majalisar Kano ranar 15 Ga Disamba, bayan wanda ke kan kujera, Abdul’Aziz Gafasa ya sauka.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *