Ƙasar China ta bayyana sassauta dokar data haramtawa al’ummar ƙasar haihuwa sama da ƴaya biyu zuwa ƴaƴa uku.
Wannan sabuwar dokar na zuwa ne bayan makonni uku da gudanar da ƙidaya a ƙasar daya ke nuna an masu ƙaranci haihuwa a tsakanin al’ummar ƙasar ta China. A sakamakon ƙidayar ya nuna a shekarar data gabata an haifi jarirai guda miliyan goma sha biyu kacal wanda shine sakamako mafi ƙaranci tun shekarar 1960
A shekarar 2016 China ta sassauta dokar haihuwar ɗa ɗaya da aka amincewa kowanne ɗan ƙasa zuwa ƴaƴa biyu kacal.
Shugaban ƙasar Xi Jiping ya amince da wannan sabuwar dokar a yau bayan kammala wani taro na musamman a birnin Beijing.