Ma’aikacin Kashe Gobara ya ceto mata da miji a Hotel, ya ga ashe matarsa ce
Ana bikin duniya ne dai ake ce akan yi na kiyama,
Sai dai an ce rashin sani ya fi dare duhu, domin daya daga cikin ma’aikatan kashe gobarar ya yi kicibis da mai dakinsa yayin da ya je ceto wasu mata da miji da gobarar ke kokarin lamushewa.
A wani bidiyo da aka yayata a kafafen watsa labaran zamani, an ga yadda wasu ma’aikatan otal ɗin ke neman agaji, yayin yan Kwana-kwana biyu ke kokarin balla dakin otal din.
Bayan da aka balla kofar ne kana aka yi nasarar ceto mutanen biyu dake cikin dakin, kwatsam sai ɗaya daga yan Kwana-kwanan ya fahimci cewa matar dake tare da namijin fa ashe matar sa ce.
To sai dai ko da ya tambaye ta abinda take yi a otal din, nan da nan ta fara neman gafarar shi saboda da sanin girman abin da ta aikata.
Faifan bidiyon ya janyo cece-kuce a shagukan sada zumunta, inda wasu ke nuna shakkun al’amarin tare da danganta hakan da wasan kwaikwayo, yayin da wasu kuma ke cewa mutanen duniya za su iya yin abinda ya fi wannan
2 Comments