Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Jahar Borno ta bayar da umarnin kulle Manyan Makarantun Jahar guda biyu, biyo bayan rikici daya afku, zuwa nan da makonni biyu masu zuwa.

Makarantun da umarnin daya shafa sun hada da; Kwalejin Ilmi ta Kashim Ibrahim Maiduguri da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibn Ibrahim El Kanemi, Bama.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ilmi na Ma’aikatar Ilmin Manyan Makarantu, Mr Muhammed Abatcha ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, yana Mai bayyana cewa an dauki matakin domin hana fantsamar rikicin wanda ya afku sakamakon Dakunan Kwanan Dalibai.

” Bayan tattaunawa da Shuwagabannin Makarantun, Ma’aikatar Ilmi ta bayar da umarnin kulle Manyan Makarantun guda biyu zuwa Makonni biyu.

Idan dai ba’a manta, ta’addan ci ne ya sanya Gwamnatin Jahar ta mayar da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibrahim El-Kanemi domin zaunawa tare da yan Kwalejin Ilmi ta Kashim Ibrahim.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *