Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Zaratan yan wasan Express Radio wato express united sunyi.kaca kaca da yan wasan kwallon kafa ta aminci radio a wani wasan sada zumunta ta suka fafata a filin wasa na azman, da ci 5-3

Tun da fari aminci radio ce ta shiga gaba a farkon wasan daci 3 amma kungiyar express karkashin jagorancin ango Abbas Musa sheka tayi kukan kura tare da warware kwallayen 3 inada ta kara 2 kwallayen suka zama 5 yan wasan da suka harda da Sani Abdurazak Darma, Amiru Inuwa Kachako, Muktar Haruna Maikananzir Abdullahi Tanko Kyaure, Nura Aliyu da Abubakar Sale Yakub sun taka rawar gani tare da fidda marada kunya a wasan taya marnar auren fitaccen dan jarida Abbas Musa Sheka,

 

Da yake jawabi kan wasan shugaban gidan radio express Alhaji Ali Baba Kusa ya jinjinawa yan wasan bisa Jamijin kokari da suke na fidda gidan radiyon kunya a kowane lokaci irin wannan inda yace hukumar gidan radiyon na sane da irin kokarin da yan wasan sukeyi a gurin ayyukan su da filin wasan kamar yadda sukayi a wannan wasan,

Ali Baba Kusa wanda yace Aminci Radio yar Uwace ga express radio ya yabawa yan wasan na Aminci bisa halin karamci da da’a da suka nuna yayin gudanar da wasan,

Daganan sai taya ango Abbas Musa Sheka fatan alheri bisa daurin auren sa inda yace yana alfahari da yadda maaikatansa ke samun karuwa inda maza da mata maaikatan radiyon ke samun damar yin aure kusa duk bayan watanni kadan abin da yake nuni da irin yadda radiyon ke rainon matasa dake alfahari da jin dadi a kafar yada labaran ta Express Radio abinda ke basu damar samun abokan zama, inda yace ” ina jin dadi da alfaharin ganin ya’ya’ ye da maaikatanmu ke zuwa dasu duk lokacin da muke wani taro kuma duk suna wannan tasha sukayi aure har Allah ya azutasu da yayaye wannan abin jin dadine” inji Alhaji Ali Baba Kusa

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *