Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ya zuwa yanzu ba a san inda Shekau yake ba tun bayan samun rahotannin da ke cewa ya mutu sakamakon wata fafatawa tsakanin dakarunsa da kuma na ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram.

Wato jama’a tun ba yau ba ake ikirarin cewa Shugaban yan ta’addan Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu.

Ga jerin lokuta biyar da aka ce Shekau ya mutu.

1) A shekarar 2009, An yi ta maganganu game da mutuwarsa sakamakon mummunan hari da sojoji suka kaddamar. Kodayake an yi ikirarin cewa harin ya murkushe masu tayar da kayar baya da yawa a lokacin, amma Shekau ya sake bayyana a yanar gizo, a wannan karon a matsayin sabon shugaban kungiyar.

2) Shekaru hudu bayan nan, wato a shekarar 2013 Rahotanni sun ce Shekau ya samu munanan raunuka daga harsasai a lokacin artabu da sojojin Nijeriya a watan Agusta, kawai sai ga shi ya bugi kirji a watan Satumba cewa ba a kashe shi ba.

3) Bai tsaya a nan ba, wani ikirari da majiyoyin Sojojin Nijeriya suka yi wanda ya samu goyon bayan wasu mutane daga rundunar sojan Kamaru sun ce da gaske ne mai laifin da ake nema ya mutu a Kodunga yayin yakin kwana biyu a shekarar 2014. Sai dai kuma, ya fito ya karyata labarin.

4) A shekarar 2015, Shekau cikin alfahari ya karyata rahoton da marigayi shugaban Chadi, Idriss Derby ya gabatar a baya cewa sabon shugaban kungiyar ta’addacin ya bayyana bayan zargin mutuwarsa.

5) A shekarar da ta biyo baya wato a shekarar 2016, Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ba da sanarwar cewa an kashe shugaban yan dan ta’addan boko haram Abubakar shekau tare da wasu jiga-jigan yan ta,addan a cikin jihar Borno. Wanda kuma bai zama gaskiya ba kamar yadda aka ganshi ba da daɗewa ba a cikin bidiyon Youtube yana barazanar tada zaune tsaye.

A halin da ake ciki yanzu, mun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan ta,addan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.

Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.

Wasu majiyoyi sun ce daruruwan yan ta,addan ISWAP sun mamaye dajin Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau shugaban yan ta,addan Boko Haram.

Wata majiya ta daban ta sanar da cewa Abubakar Shekau shine ya hallaka kan shi da kan shi sakamakon cimmasa da ya ga ‘yan ta’addan ISWAP sun kusa yi a maboyar shi dake cikin dajin Sambisa.

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *