- Shugabancin kungiyar magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta kano pillars ya jinjinawa kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa bisa irin hangen nesa da kyautata muamala tsakanin sa da kungiyar,
Shugaban kungiyar na kasa Bashir Idris Muazu Jide ne bayyana haka yayi mika wata kyautar girmamawa da kungiyar ta shiryawa dan wasan a ranar lahadi a wasansa na farko da zai buga tun bayan dawowarsa kungiyar daga Al Nasr na kasar saudiyya
Bashir Jide wanda yace shawarar da Ahmed Musa ya yanke na dawowa kungiyar kano pillars duk da irin daukaka da Allah yayi masa a fagen wasan wani abune da yake da wuya a wajen yan wasa irinsa in banda kyakkyawan halinsa daya saba dana sauran,
Jide ya kara da cewa dawowarsa kungiyar kano pillars ya sake fito da sunan kungiyar a idon duniya inda jaridu da kafafen yada na duniya wanda hakanma wata martabace da ba kowace kungiyace ke samun irinta ba,
Da yake tsokaci kan kyautar da kungiyar ta bawa dan wasan Bashir Jide cewa yayi tun dama can akwai kyakykyawar alaka tsakanin dan wasan da kungiyar magoya bayan tun zuwansa kungiyar sama da shekaru 16 da suka gabata inda yace wannan wata damace da zata sake nunawa dan wasan cewa har yanzu akwai wannan alakar kuma su nuna masa jin dadinsu na sake dawowa kungiyar da dan wasan yayi,
Ahmed Musa ya fara buga wasansa na farko da kungiyar Adamawa United a garin Kaduna inda take matsayin gida ga kungiyar kano pillars tun bayan gaza samar da filin wasa ga kungiyar da gwamnatin jihar kano tayi sakamakon rufe filin wasa na sani abacha saboda cutar corona da kuma kasa gyara filin wasa dake sabon gari abin daya sanya dole kungiyar biyan kudin hayar filin wasa a Kaduna dan buga wasanninta na gida.