Ayayin da ake daf da kammala azumin watan ramadana kuma ake tunkarar biking karamar sallah zakkatil fitr na Daya cikin abubuwan da musulmi kan fitar ga mai iko Dan bawa mabukata, kan hakane fitaccen malami sheik Aminu Daurawa yayi tsokaci kan matakai da shrarudai na zakkar fidda kai ga kuma yadda ya karkasa kaidoji da sharuddan.
ZAKKAR FIDDA KAI TANA DA SHARAƊI HUƊU
Na farko: Mai bayarwa ya zamo Musulmi.
Na biyu: Ya kasance mawadaci.
Na uku: Ya zamo an ba da ita a kan lokaci.
Na huɗu: A bada ita ga wanda ya cancanta.
WAƊANDA ZAKKAR FIDDA KAI TA ZAMA WAJIBI A KANSU
Wannan zakka tana zama wajiba a kan kowani Musulmi babba da yaro, mace da namiji, tsoho da tsohuwa, ɗa da bawa.
MATAKAN DA AKE BI WAJEN FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI GUDA UKU NE
Ya halatta a bayar da ita kafin zuwan ranar Idi da kwana ɗaya ko biyu.
Lokacin fitar da zakkar fidda kai yana farawa ne daga faɗuwar ranar ashirin da tara (29 ga watan Ramadan zuwa kafin a tafi sallar Idi.
An so a fitar da wannan zakka ranar SAllah kafin a tafi Idi. Ba ya halatta a jinkirta ta har sai an dawo Idi.
Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne gwargwadon kwano ɗaya, wato mudannabi huɗu kenan.
NAU’IN ABINCIN DA AKE BAYARWA
A zakkar fidda kai ana bayar da kowani nau’in abincin da mutanen garin suke amfani da shi, kamar dangin su alkama, shinkafa, gero, dawa, masara, da wake. Amma an fi so a bayar da abin da mutum zai iya sarrafawa ya ci cikin sauƙi, kamar shinkafa, alkama ko filawa.
WAƊANDA AKE BA ZAKKAR FIDDA KAI SU NE TALAKAWA DA MISKINAI
Wasu malaman suna ganin ya halatta a zakkar fidda kai mutum ya bayar da kuɗi maimakon abinci, amma idan wanda za a ba ya fi buƙatar kuɗin, wataƙil wani ya ba shi abincin amma ba kuɗin dafawa.
Wajibi ne idan ka fitar wa kanka zakkar fidda kai, sai kuma ka fitar wa da ‘ya‘yanka da matarka da waɗanda ke ƙarƙashinka idan ba su da hali.
Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne a garin da ake zaune sai dai idan duka garin masu arziƙi ne shi ne za a iya fitar da ita wani garin daban.