Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci Kaddamar da Manufofin Kasa don Inganta hanyoyin sashin sadarwar Nijeriya da Ingantaccen manufofin kasa na Dijital kan Rajistar katin Sim Card a fadar shugaban kasa a yau Alhamis 6 ga watan Mayu 2021.
Shugaba Buhari ya amshi katinsa na shaidar zama dan kasa NIN a hukumance daga Ministan Sadarwa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, yayin da yake jagorantar kaddamar da Manufofin Kasa don Inganta hanyoyin sashin sadarwar Nijeriya da Ingantaccen manufofin kasa na Dijital kan Rajistar katin Sim Card.
Shugaba Buhari tare da Shugaban Hukumar Gudanarwa na Hukumar Sadarwa ta Najeriya Farfesa Adeolu Akande, Ministan Sadarwa Dr. Ali Isa Pantami da SGF Boss Mustapha tare da sauran shugabannin hukumomin Sadarwar a wajen Kaddamar da sabbin Manufofin sadarwar don cigaban kasa.