Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar sojin Najeriya bayyana cewa mutumin da ‘yan sandan Kaduna ke tuhuma Adamu Galadima da laifin sace dan makwaucin sa da kashe shi bayan karbar kudin fansa ba ma’aikaci bane, wato ba soja bane.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Mohammed Yerima ya bayyana cewa Galadima ya yi aiki da rundunar sojin Najeriya amma an sallame shi tun a shekarar 2013.

Ya ce Galadima ya samu aikin shara da ma’aikatar muhalli bayan da ya bar aikin soja.

Idan ba a manta ba a baya Jaridar Dimokuraɗiyya ta buga labarin yadda rundunar ‘yan sandan Kaduna ta kama wasu matasa uku da mace daya da suka yi garkuwa da yaron dan shekara 6 a unguwar Badarawa dake Kaduna.

makwabcin yaron ne ya sace shi Kuma ya mika wa gogarman su arce da shi Kano.

Daga baya suka nemi mahaifin ya biya kudin fansa naira miliyan 1.

Maimakon su maido masa da yaron sai daya daga cikin su ya ce yaron ya gane su fa kuma zai iya tona musu asiri idan ba su dau mataki ba.

Daga nan sai suka yanke shawarar su kashe yaron kawai su ja bakin su su yi shiru.

Bayan haka wasu mutane sun yi korafin cewa daga daga cikin gogarman da suka yi garkuwa da yaron soja ne.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *