Gwamnan Jahar Oyo Seyi Makinde a jiya ya bayyana cewa rashin kyakkyawan shugabanci da Jami’iyyar APC take yi, bazai wuce Shekarar 2023, yana mai cewa yan Najeriya sun gaji da Jami’iyyar, kuma zasu koreta daga mulki idan zabe yazo.
Gwamna Makinde wanda ya bayyana haka a lokacin taron kaddamar da shuwagabannin Jami’iyyar PDP na yankin Kudu Maso Yamma wanda ya gudana a gidan Gwamnati dake Agodi, Ibadan, yace tabbatar da nasarar Jami’iyyar PDP ya fara daga yankin Kudu maso yamma.
Makinde a cikin jawabin daya fitar a tabakin Sakataren Labaran shi Mr. Taiwo Adisa yace hadin kain Jami’iyyar PDP shi zai kara bata nasara a yankin kudu maso yamma da kuma Najeriya baki daya.Jami’iyyar APC bazata kara mulkar Najeriya bayan Shekarar 2023>>>inji Makinde