Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 18 ga Fabrairu ne za a gudanar da Babban Zaɓen shekarar 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin jawabin da ya gabatar wajen taron dandalin sauraron jama’a a kan Ƙudirin ƙirƙiro Dokar kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa wanda Kwamitin Hukumar Zaɓe na Majalisar Dattawa ya shirya a Abuja.

Farfesa Yakubu ya ce: “Wannan Hukuma ta ƙosa ta san irin dokar da za ta yi aiki da ita wajen aiwatar da manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023. A bisa ƙa’idojin da Hukumar ta kafa, za a gudanar da manyan zaɓuɓɓukan 2023 ne a ranar Asabar, 18 ga Fabrairu, 2023, wanda ya kama shekara ɗaya da wata tara da mako biyu da kwana shida daidai daga yau ɗin nan ko kwanaki 660.”

Shugaban ya ce shekaru 13 bayan shawarar da Mai Shari’a Muhammadu Lawal Uwais ya bayar kan a kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe (National Electoral Offences Commission), da kuma wasu rahotannin kwamitoci daban-daban a kan batun, “a yau ga mu a wajen wannan taro na tarihi domin mu bada namu shawarwarin kan wannan doka.”

Ya ce, “Ba shakka, an ɗora wa INEC ayyuka masu yawa domin ana yin zaɓuɓɓuka a sassan Nijeriya a duk tsawon shekara.

“Tun daga zaɓen 2015, an gudanar da shari’u 124 kan laifuffukan zaɓe amma a guda 60 kaɗai ne aka yanke hukunci.”

Ya ƙara da cewa: “To amma, a yayin da mu ke jin daɗi game da wannan taron na yau, mu na kuma so a fito da tsarin doka mai suna Dokar Zaɓe (Gyararriya) wanda a kan ta za a aiwatar da zaɓuɓɓukan 2023, wanda za a yi a ranar 28 ga Fabrairu, 2023, kuma a rattaba hannu a kan ta a kan lokaci.”

Tun da fari, sai da Shugaban Kwamitin Hukumar Zaɓe na Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya bada tabbaci ga dukkan masu ruwa da tsaki cewa Ƙudirin Dokar Zaɓe (Gyararriya) na 2021 ya na samun kulawa kuma ana fatan Shugaban Ƙasa zai rattaba hannu a kan ta.

Gaya ya ce ba shakka kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa “zai canza labarin tsarin mu na gudanar da zaɓe.”

Wanda ya kawo ƙudirin kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce an fara ƙudirin kafa hukumar ne tun a Majalisar Dattawa ta 8 lokacin da ya kawo shawarar ƙudirin tare da Ovie Omo-Agege saboda sun fahimci cewa INEC ba ta iya hukunta ko da kashi 1 cikin ɗari na laifuffukan zaɓe, saboda haka akwai buƙatar a ɗauke wannan aikin daga kafaɗun ta, a bar ta ta yi aikin ta da kyau.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *