Yadda musulunci ya shigo mana wannan kasa, tarihi ne mai tsawo, wanda yake komawa tun a lokacin Sahabbai ko Tabi’ai. Saboda haka, tarihi ba zai manta da Ukuba Ibn Nafi’u ba, Sahabi mai daraja wanda ya sanya kafarsa a cikin Afirka.
Idan an koma baya in muka dubi umurnin da manzon Allah (S.A.W) ya bai wa sahabbansa sama da mutane saba’in da biyu su yi hijira ta farko zuwa kasar Ethiopia (Habasha) da kuma na hijira ta biyu sama da mutane arba’in zuwa Habasha har wa yau.
Wannan tawagar ta kunshi maza da mata. A lokacin sarkin Habasha shi ne Najjashi wanda shi mabiyin addinin Kirista ne. Bayan sun gama zamansu a Habasha sun bar mutane da yawa a Habasha saboda sarkin ya karbe su hannu bibbiyu bai yi kyamar su ba, su kuma ba su yi kyamar sa ba. Wannan kaunar tana da babban matsayi a tarihin musulunci domin tana koyar da abubuwa kamar haka:
Zamantakewar musulmi da wanda ba musulmi ba musamman mabiya addinin Kirista.
Kuma wannan na nuna alaka tsakanin kasar Makka da Afirka.
Haka kuma wannan na nuna cewa musulunci ya shigo kasar Afirka kafin ya shiga Madina.
Sannan tarihi ba zai manta da tabi’i Ziyad Ibn Tariq ba, wanda ya gangaro da musulunci gabar Afirka ta Yamma. A sakamakon haka har muka samu isowar musulunci a wannan kasa tamu Nijeriya a yanzu.
A game da Nijeriya, tarihi ya nuna mana ba a shigo mana da musulunci ta hanyar karfi ba. A’a musulunci ya shigo mana ne ta hanyoyin fataucin kasuwanci da kuma matafiya na sa-kai don neman tarihin kasa da da’awa ta wa’azi da kuma hanyar kaurace-kaurace na kabilu da al’ummu daga wuri zuwa wuri kamar yadda ya gabata.
Dubi: Yadda aka fara rubuta kagaggun littattafaina Hausa
‘Yan kasuwa
‘Yan kasuwa su ne suka fara shigowa da musulunci kasar nan, amma ta hanyar daidaikun mutane ne. Wasu ma suna ganin tun a farkon karni na Hijirar Manzon Allah (S.A.W) musulunci ya fara saduwa da kasar Hausa ta gefen Katsina zuwa Kano, inda matafiya na kasuwanci suke bi daga wasu kasashe na Larabawa. Su ne kuma suka shigo mana da musulunci ta wannan hanyar zuwa arewacin Nijeriya.
Matafiya
Sannan hanya ta biyu ita ce ta wurin matafiya don rubuta tarihin kasa kamar su Ibn Khaldun da masu wa’azi kamar su Al-Maghili. Ta wannan fuskar sun fi mai da hankalinsu ta saduwa da sarakuna da mahukunta da malamai.
A wannan hanyar ta biyu sun zo ne daga baya, kuma sun samu kasar Hausa cike take da mabiya addinin musulunci musamman ma talakawa. Watau dai a takaice talakawa sun fara karbar musulunci a kasar Hausa kafin sarakunansu su karbe shi. Misali, sarkin Katsina Korau (1320-1353) shi ne ya fara karbar addinin musulunci, sai sarkin Kano Yaji (1349-1385) wanda Wangarawa suka zo a lokacinsa, suka shigar da shi addinin musulunci. Sai sarkin Zazzau wanda ya musulunta na farko cikin sarakunanta shi ne Muhammadu Rabo. A masarautar Zamfara kuwa musulunci ya fara shigowa ne shekara ta 1640 A.D.
Amma an ce kasar Zamfara ta karbi musulunci kafin 1640 A.D shi ne ingatacce. Haka dai sarakunan suka rika musulunta suna karfafa Hakimai da Dagatai nasu a cikin musulunci da masu unguwanninsu har zuwa ga talakawa.
Misali, a zamfara akwai wasu malamai wadanda ake kira malamai na ‘Yan Doto. Su wadannan malamai suna kasar Zamfara tun shekaru aru-aru kafin bayyanar Shehu Usman dan Fodiyo. Wadannan malamai su ne ake kyautata zaton cewa su suka rubuta wasu shahararrun littattafai ‘yan kanana cikin Ilmin Fiqhu da Tauhidi da sauransu. Kamar littafin Qawa’idi da Rashada da Ma’anar La’ilaha illallahu Muhammadur- Rasulullahi da makamantansu.
Daga Tsumagiya.com