Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

An haifi Janar Muhammadu Buhari ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura, sannan Tauraruwar Janar Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka ba shi mukamin ministan man fetur da ma’adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo.

Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan sabuwar Jihar Arewa maso Gabas da Janar Murtala Ramat Muhammed ya kirkiro.

Daga bisani kuma aka nada shi shugaban hukumar NNPC wadda aka fara kafawa a shekarar 1977.

A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada shi shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kudaden rarar man da kasar ta samu a wannan lokaci domin gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.

Kuma ayyukan da Janar Buhari ya yi wa Nijeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu ya sa wasu ‘yan Nijeriya son ganin ya sake zama shugaban kasar.

Sau biyu Janar Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugaban kasar karkashin tutar jam’iyyar ANPP wato 2003 da 2007, wadanda duka bai samu nasara ba.

Rashin nasarar da ya yi karo biyu bai sauya masa ra’ayi ba game da siyasa a Nijeriya, kuma tuni ya kaddamar da tashi jam’iyyar da ya kira CPC wadda yake takarar shugaban kasa a zaben da za’a yi a shekarar 2011.

Tsohon Sojan, Dogo, Siriri, wanda aka haifa a garin Daura mai cike da tarihi da ke arewacin Nijeriya, shekaru 72 da suka wuce, ya yi suna ne a shekarar 1983, a lokacin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hulla.

A matsayinsa na soja mai mulkin kama-karya a lokacin, ya zama mutumin da ke nuna ba-sani-ba sabo wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ya kulle ‘yan siyasa masu yawa da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Tuni dai Muhammadu Buhari ya bayyana kansa cewar yanzu shi ma ya rungumi dimokuradiyya.

Ya samu nasara ne tare da gagarumin rinjaye a zaben da masu sa ido suka ce shi ne ya fi kowanne inganci wajen nuna adalci a kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Ya kuma samu wannan nasara ce, bayan da ya sha kaye a zabubbuka uku a baya.

‘Mukamai’

Muhammadu Buhari, ya dare kan karagar mulki ne da dumbin gogewa a harkokin mulki, bisa la’akari da irin manya manyan mukaman da ya rike a gidan soja da kuma waje, wadanda suka hada da gwamnan, da ministan albarkatun mai da kuma uwa-uba shugabancin Nijeriya karkashin mulkin soja.

Buhari mutum ne da ya sha banban da sauran akasarin shugabannin Nigeria, saboda bai tara wata dumbin dukiya ba, duk kuwa da irin wadannan manya manyan mukamai da ya rage.
Akasarin jama’a a Nigeria sun yi shaidar sa a kan mutum mai rikon amana.

Ya karbi mulki ne a wani yanayi na tsuke bakin aljihu saboda faduwar farashin mai da kuma raunin tattalin arziki wanda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.

‘Tsaro’

Babban kalubalen da ya fi bukatar sa ido, shi ne yakin tsawon shekaru da Nijeriya ke yi da kungiyar Boko Haram wadda ke da alaka da kungiyar IS a sashen arewa maso gabashin Nigeria.

Yakin dai ya yi sanadiyyar hallaka mutane fiye da dubu goma sha biyar, yayin da ya tagayyara wasu fiye da miliyan daya da rabi daga gidajensu.

Wannan dai shi ne zai kasance karo na biyu da tsohon shugaban mulkin soja a Nijeriya yake a matsayin shugaban farar hula.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *