Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan yan sanda Alhaji Sanusi Buba sun yi nasarar hallaka yan bindiga ukku har lahira a daren jiya Lahadi a kauyen Marabar Gurbi da ke karamar hukumar Kankara tare da cafke yan bindiga Biyu da suka kashe wani dan kasuwa Alhaji Ibrahim Kwatahi da ke kauyen Jargaba da ke cikin karamar hukumar Bakorin Jihar Katsina.

Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyanawa manema labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina.

Gambo Isa ya kara da cewa wadanda aka hallaka har lahira an samu bayanan sirri cewa yan bindiga za su biyo ta wani burtali da shanun da suka sato, baturen yan sanda ya jagorancin jami’an tsaro, inda suka yi masu kwantar-bauna, nan take suka hallaka ukku daga cikin su, sauran sun tsere daji da halbin bindigar a daji. A cikin binciken da ake an samu bindiga kirar Ak49 guda daya da shanu guda dari da sittin da tumaki dari da saba’in da mashina guda biyu a hannun su.

SP Gambo Isa ya ci gaba da cewa rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke Buhari Yusuf dan shekara ashirin da biyar da haihuwa da Usman Alhaji Bammi dan shekara talatin dake Unguwar Mai Kawo a cikin karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina, wadanda su ne suka kitsa harin da aka kashe wani Ibrahim Fatahi da ke kauyen Jargaba a karamar hukumar Bakori.

Haka zalika, rundunar ta yi nasarar wani mai Shahararren mai safarar alburasai, Ibrahim Ma’aruf wanda aka fi sani da Risku dan shekara 40 da haihuwa dake kauyen Tashar Bokiti a gundumar Runka ta karamar hukumar Safana a jihar Katsina. An kama shi tsakanin hanyar Dutsinma zuwa Safana dauke da shanun sata arba’in da alburasai 96 na bindigar kirar Ak47 da zunzurutun kudi har naira dubu dari bakwai da tamanin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *