Gwamnatin jihar Kebbi ta karbo dala milyan saba’in daga Bankin duniya domin bankasa ilmin mata, inda za a yi amfani da kudin wajen koyar da su a fannoni daban-daban na harkar ilmi.
Gwamna Bagudu tyaci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa mata domin idan ka gina mata tamkar ka gina al’umma ne maki daya.
Bagudu ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki ya fitar, inda ya kara da cewa Bagudu ya ce “Yawan taimakon da za mu iya bai wa mata yanayin yadda al’umarmu za ta habaka”.
Bagudu ya bayyana mata a matsayin wadanda duk wahalar da aka sha ta annobar korona ta matsin tattalin arziki ta kare a kansu.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wata makala da jihar ta shirya wa mata domin zuwan watan Ramadana, wadda aka yi wa taken “Muhimmiyar rawar da mata za su iya taka wa a Musulunci.”
Gwamna Bagudu ya kuma yabawa mai dakinsa Dakta Zainab Shinkafi Bagudu da sauran wadanda ke da hannu wajen hada lakcar.
A yayin jawabin ta, Matar Gwamnan Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, wadda ita ce jagorar taron, ta bayyana cewa babbar nasarar da za a iya samu a wannan lokaci na Ramadan ya danganta da irin gudummawar da mata za su bayar ba a iya gidajen su kadai ba har da cikin al’umma.
Ta kuma jawo hankulan al’umma da su ribanya ayyukan alkairan su ta hanyar yawaita sadaka, ayyukan alkari ga al’ummar yankin sa, domi kebe matasa daga mugayen ayyuka musamman bayan sallar turawi.
Tun a farko, mai baiwa Gwamna shawara kan harkokin mata a jihar Kebbi, Honarabul Zara’u Wali ta yabawa Dakta Zainab Shinkafi Bagudu kan hada lakcar.
Wasu daga cikin wadanda suka yi jawabi a wurin taron sun hada da Sheikh Abubakar Giro, wanda Dr. Attahiru Ahmad Sifawa ya wakilce shi, sai Dr. Isma’il Mufti-Menk, Na’ima Robert da Dr. Jabir Maihula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon kakakin majalisar tarayya, Rt. Hon. Dimeji Bankole, kakakin majslisar dokokin jihar Kebbi, Rt. Hon. Samaila AbdulMuminu Kamba, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu (Jarman Kabi), SSG, Babale Umar Yauri da kuma shugaban ma’aikatan gwamnati, Alhaji Safiyanu Garba Bena da sauransu.
Makalar dai ta mayar da hankali ne kan yadda mata za su tafiyar da gida a lokacin annobar korona, wajibin da ke kan mata na kula da iyali a yayin matsin tattalin arziki da kuma yadda za a kawo karshen cin zarafin mata