Wata kwararriyar likitan bangaren abinci a Babban Asibitin Agege dake jihar Legas, Olufunmilola Adewumi ta shawarci masu bukatar karin ni’ima da karfin sha’awa da su dage da shan rake.
Kwararriyar likitar ta ce shan raken zai iya taimaka wa mata masu matsalar ciwon mara samun sauki yayin daukar ciki da kuma samun saukin haihuwa.
A cewarta, rake na dauke da isassun sinadaran kara ni’ima kamar vitamin C da vitamin B2 da magnesium da iron da potassium da kuma phosphorus.
Ta ce, “Rake na dauke da sinadaran da ke kare jariri a cikin mahaifiyarsa daga cututtuka da dama.
“Tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin gaba da kuma kara ruwan maniyyi.
“Tana taimakawa wajen rage matsalar kankancewar gaba,” inji likita Olufunmilola.
Ta ce baya ga wadannan fa’idojin, shan rake a-kai-a -kai na taimakawa wajen takaita tasirin cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.
“Ta kan rage cututtukan da ke da alaka da mafitsara da koda da kuma duwatsun ciki, musamman in aka had ata da lemon tsami da ruwan kwakwa,’’ inji ta.
Daga nan sai ta shawarci a rika shan akalla mililita 400 na raken a kullum domin samun cikakkiyar fa’idarta.
Sai dai ta yi gargadi kan cewa shan raken fiye da kima na iya rikita ciki, ya kawo rama, ciwon kai da kuma yawan jin bacci.