Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cafke mutum 10 da take zargi hannu dumu-dumu a rikicin ‘yan kungiyar asiri a Ikere Ekiti da ke karamar hukumar Ikere a jihar Ekiti wanda ya jawo asarar rayukan mutum shida (6).
Jami’in watsa labarai na hukumar ‘yan sandan, ASP Sunday Abutu wanda ya tabbatar da faruwar hakan wa ‘yan jarida a Ado Ekiti, yana mai cewa arangamar ‘ya’yan kungiyar asirin ya faru ne a ranar Asabar da daddare, har zuwa farkon safiyar ranar Lahadi ana tafka gumurzu.
“Zan iya tabbatar muku cewa mutum 10 sun shiga hannunmu wadanda suke da alaka da rikicin kungiyar asiri. rikicin da ya samu asali a sakamakon gabar da ke tsakanin su mai karfi.”
Kakakin ƴan sandan ya kuma tabbatar da cewa mutum shida ne suka rasa rayukansu a wannan artabun, yana mai karawa da cewa tunin aka kwashi gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki da ke asibiti.
“Nan da nan muka kaddamar da sintirin hadin gambiza na ‘yan sanda, sojoji da jami’an Amotekun da jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence.
“Wadannan da muka kama suna tsare a hannunmu kuma da zarar muka kammala bincikenmu za mu gurfanar da su gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu.”
Kamfanin Dillacin Labarai na NAN ya labarto cewa Rundunar ‘yan sanda ta kara jibge jami’anta a yankin wadanda suke aikin suntiri da tsaida ababen hawa da daidaikun jama’a domin bincike kan masu shigowa ko masu fita daga cikin yankin.