Ƴan Arewa mazauna Jihar Imo musamman Hausawa na cikin zullumi da zaman ɗar-ɗar biyo bayan kashe ƴan uwansu da ƴan ƙabilar IGBO masu rajin neman ƴan cin kai suke yi a yankin Orlu da sauran wurare daban-daban a faɗin Jihar.
Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda tsagerun na IGBO suka mamaye wasu daga cikin manyan titunan Jihar Imo ɗauke da makamai suna nufar Hausawa mazauna yankunan da hare-hare. Lamarin da kawo yanzu ya sanya wasu daga cikin Hausawan yankunan da abin ya shafa suke barin matsuguninsu domin tsira da rayukansu.
A harin na kwana-kwanan nan dai, an samu labarin yadda ƴan ƙabilar ta IGBO suka hallaka Hausawa masu sana’ar sayar da nama (Suya) a yankin Atta dake ƙaramar hukumar Ikeduru a Jihar ta Imo.
A nasa ɓangaren Shugaban Hausawa na yankin Owerri, Alhaji Sani Ahmed Mai Rago ya tabbatar da faruwar al’amarin kuma ya bayyana yanda a halin yanzu sukayi jana’izar ƴan uwan nasu da dama waɗanda al’amarin ya shafa.
Har’ilayau; Shugaban Hausawa na yankin Ama Awusa, mai suna Alhaji Auwal Baba Suleiman yayi Alla-wadai da hare-haren, wanda ya bayyana cigaba da kaiwa Hausawa hari da gangan ka iya zama silar rugujewar zaman lafiya a Jihar ta Imo dama ƙasa baki ɗaya.
Yayin jin ta bakin ɗaya daga cikin Hausawa mazauna garin na Imo, Dr Lawan Yusuf shima ya bayyana takaicin sa musamman yanda tsagerun na BIAFRA suke tsare Hausawa da gan-gan tare da neman shaidar shiga ƙasar wato (visa) da zarar kuma mutum ya gaza nuna masu shaidar, take a wurin zasu far masa “sai kuma inda hali yayi”.
A halin yanzu mutum 11 ne ake da tabbacin mutuwar su, cikin mako biyu da tsagerun suka kwashe suna kaiwa Hausawa hare-hare a yankunan na Jihar Imo; “kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa”.
Jaridar Mikiya na ƙoƙarin ƙara tattauna da wasu daga cikin Hausawa mazauna garin na Imo domin ƙarin haske; kuma da zarar an samu ƙarin bayani game da al’amarin zamuyi ƙoƙarin sanarda masu bibiyar mu.