Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A kalla ƙananan yara dubu biyar da dari biyu ne aka kwantar a asibiti sakamakon fama da cutar tamowa, wato karancin abinci mai gina jiki a Jihar Nassarawa daga watan Agustan 2020 zuwa Yanzu.

Jami’a Mai Kula da Bangaren Abinci Mai Gina Jiki a Jihar ta Nassarawa Hajiya Halima Yusuf ita ta bayyana haka yayin wani taron gangamin wayar da kan jama’a kan abinci mai gina jiki a Jihar a Jiya Juma’a.

Hajiya Halima Yusuf sa’ilin da ta tabo batun kalubalen abinci maia gina jiki daga shekarar 2014 zuwa 2020 ta ce matsalolin n ci gaba da karuwa a jihar a yan shekaru, wanda dole sai an tashi tsaye.

Ta ce cikin adadi dubu biyar da aka kwantar a asibitoci mabanbanta a Jihar, kimanin tamanin da daya sun riga mu gidan gaskiya, yayin da sama da dubu biyu Kuma ne suka samu waraka.

A bangaren Shugaban Kwamitin Harkokin Abinci da Kayayyakin Gina Jiki ta Jihar Alhaji Osama Abdul wanda kuma har ila yai shine Daraktan Tsare-tsare a Ma’aikatar Kudi ta Jihar, ya ce a yanzu haka an kebe kudi kimanin Naira biliyan uku don yaki matsaloli makamantan Wannan da a Yanzu haka sahalewar gwamnan jihar ake jira.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *