Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tun bayan sace daliban makarantar sakadiren na kankara dake jihar katsina “Gwamnatin jihar a yanzu tabada umarnin fara amfani da karnuka a makarantun jihar don fallasa Yan binduga koda sunkai samaye da niyyar yin garkuwa da dalibai ko malamai.

Kwamishinan ilimin jihar ta Katsina Prof. Badamasi Charanci ya tabbatar da bada umarnin fara amfani da karnuka a Makarantun “inda yace wannan na daya daga cikin matakan da suke dauka, ya kara da cewa “dakwai wata hikimar cewa ko wacce makaranta mutanaji karnuka domin kuwa wani zaiyi mamaki ace a tanaji karnuka, karnukan nan namu local zakaga suna shakar abinda baka iya shaka toh idan yara sunajin haushi da daddare “Security Men” sunajin haushi da daddare Yan sintiri zasu zama cewa dakwai wani abu wanda basu gani ba wannan kamar Alat ne wanda dabbobin nan zasu iya taimaka mana dasu inda babu munsa su samo inda keda akwai munsa su cigaba da tattalin su.

Bayaga irin wannan mataki akwai wasu karin matakan kare Yan makarantar daga Yan bindugar, inda hukumomi sukace an jibge jami’an tsaro a kowace makaranta dake fadin jihar kamar yadda Gwamnan jihar Aminu Bello Masari yai karin bayani akan sauran matakan da suke dauka nakare Makarantun jihar “Duk makarantar kwana mun kebe gurin kwanan munsake mashi bango, munsa waya ta tsaro sannan kuma a Makarantun mun gina abinda ake cewa “Observation Terwos” hasumiyya wadda jami’an tsaro zasu hau duk dare, sannan kuma yanzu haka muna aikin sa wuta ta hanyar rana a dukkan Makarantun nan musamman da daddare yadda zasu haskaka.

Jawabin Major Bishir Galba Mai Murabus Masanin tsaro a Najeriya “Maganar kawo karnuka dinnan na tabbata kafin sufara kawo shawarar nan sunyi nazari domin duk wani wanda kasani yana aiki ko wani dan makaranta kowane rana sai an horar zakarun nan sunsan kanshin mutanan ko warin mutanan, kuma irin wadanda karnuka dole sai sun samu mutane kwararru wanda suke basu horo, amman amfani da karnukan yana da kyau domin kuwa hakan yana iya bada gargadi kamar wadansu baki sun iso hakanan suyi iho kowani abu.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *