Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata’ala tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen hilitta muhammadu ( s.a w ) da iyalan gidansa da sahabbansa
Sayyada Hafsatu ‘Yar Sayyidina Umar
Sunanta hafsatu ‘ yar umar dan kaddab dan nufail dan abdul – uzza Mahaifiyar ta itace zainab’yar maz’un dan habib dan wahabi dan huzaifata , Sayyada hafsatu shakikiyar abdullahi dan umar ce.
Ta auri Manzon Allah, bayan rasuwar . Mijin ta khunaisu dan huzaifata ( As – Sahamiyyu , Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , yana ganin girmanta da na mahaifinta da kuma mijinta , gwarzon shahidi . Sayyadina Umar ( R.A ) ya ce : ‘ Na hadu da ( Sayyadina Usman ) na yi masa maganar Hafsatu , sai ya ce min , in dan jira . Bayan mun hadu da shi bayan wasu
kwanaki sai yace min ba zai iya aure yanzu ba Sai na hadu da Sayyadina Abubakar ( R.A ) , sai na ce masa ‘ in kana so zan Aura maka Hafsatu . Sai Sayyadina Abubakar ( R.A ) ya yi shiru bai ce komai ba . Sai Sayyadina Umar ya ce , an dan samu wasu ‘ yan kwanaki bayan yin hakan , Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , ya nemi aurenta , ya kuma aurenta . Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , ya auri Sayyada Hafsatu , a cikin watan Sha’aban , shekara uku da yin Hijira . Sayyada Hafsatu ta tare a dakinta , ta zauna tare da sauran ‘ yan uwanta , matan Manzon (S.a.w) Allah Sallallahu Alaihi sai Manzon Wasallama
Sayyada Hafsatu ta tsaya tsayin – daka akan nasihar da mahaifinta Sayyadina Umar ( R.A ) ya yi mata , akan cewa ta yi biyayya ga mijinta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , kada ta saba masa cikin duk abin da ya umarceta . Sannan kada ta nuna kishinta ga ‘ yan uwan zaman auranta , Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , ya saki Hafsatu , a lokacin Sayyadina Umar ya rasa yadda zai yi , sabo da tsoron kada ‘ yarsa ta ja masa fushin Allah dana Manzonsa . Bayan wayewar gari , sai Allah Ya aiko Mala’ika Jibrilu ( A.S ) wajen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama , yace masa : Allah madaukakin Sarki yana umartarka da ka mai da Hafsatu , saboda jin kai ga Sayyadina Umar ( R.A ) .
WAFATIN SAYYADA HAFSATU ( RA ) Sayyada Hafsatu ta rasu a Madina , a shekara ta 45 bayan Hijira . An rufeta makabartar Baki’a , shekarunta a lokacin 60 . Mamrwan dan Hakam shi ne yayi mata sallah , kuma ya raka ta har makabarta , yana Nan aka Rufe ta Wadanda suka sa ta a kabari su ne , Abdullahi dan Umar da Asir dan Umar da Hamnata dan Abdullahi dan Umar da Ubaidullah dan Abdullahi dan Umar . Ta lokacin khalifancin Sayyadina Usman ( R.A )